IQNA

Cibiyar Gyaran Littafai Ta Hubbaren Abbas (AS) Ta Gyara Daruruwan Littafai A Cikin Shekaru 10 Da Kafa Ta

23:50 - February 13, 2021
Lambar Labari: 3485647
Tehran (IQNA) cibiyar da ke kula da gyaran tsoffin littafai da ke karkashin hubbaren (AS) ta gyara daruruwan kwafin littafai a cikin shekaru 10 a Iraki.

A cikin shekaru 10 da kafa cibiyar da ke kula da gyaran tsoffin littafai da ke karkashin hubbaren (AS) cibiyar ta samu nasarar gudanar da ayyuka na gyaran daruruwan kwafin littafai da suka rududduge saboda jimawa.

Akil Abdul Hussain Alyasiri shi ne shugaban wannan cibiya, a wata zantawa da ta hada shi da tashar talabijin ta Alkafil ya bayyana cewa, hakika wannan nasara da suka samu sakamako ne na aiki tukuru da ma’aikatan cibiyar suke yi, wajen ganin sun bayar da gudunmawa a wannan fage da suke da kwarewa ta musamman.

Daga cikin ma’aikatan da suke gudanar da aikia  karkashin wannan cibiya dai akwai malamai wadanda suke da masani a kan almomin da suke cikin irin wadannan littafai, sai kuma kwarraru daga jami’oi wadanda suke da masani a wannan fanni.

Baya ga littafai na ilimin da aka rubuta wasunsu daruruwan shekaru da suka gabata, akwai wasu daga cikin dadaddun kwafin kur’ani mai tsarki da aka yi gyaransu a wannan cibiya.

3953691

 

 

 

 

captcha