IQNA

Tsohon Jakadan Amurka A Yemen:

Iran Da Saudiyya Za Su Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kawo Karshen Yaki A Yemen

23:29 - February 14, 2021
1
Lambar Labari: 3485651
Tehran (IQNA) tsohon jakadan kasar Amurka a kasar Yemen ya bayyana cewa, kasashen Iran da Saudiyya za su iya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen yakin kasar Yemen.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, tsohon jakadan jakadan kasar Amurka a kasar Yemen Gerald Michael Feierstein ya bayyana cewa, kasashen Iran da Saudiyya za su iya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen yakin kasar Yemen, bisa la’akari da irin tasirin da suke da shi.

Gerald Michael Feierstein wanda ya kasance jakadan Amurka a kasar Yemen a shekara ta 2010 zuwa 2013, a lokacin mulkin Barack Obama, ya zama mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka a kan harkokin yankin gabas ta tsakiya daga shekara ta 2013 har zuwa karshen shugabancin Obama.

Ya ce saka kungiyar Ansarullah ko kuma Alhuthy a cikin jeren kungiyoyin ‘yan ta’adda da gwamnatin Trump ta yi babban kuskure ne, domin kuwa hakan yana da babbar illa ga rayuwar al’ummar kasar Yemen.

Baya ga haka kuma ya yi ishara da irin matsanancin halin da al’ummar kasar ta Yemen ta shiga, sakamakon yakin da gwamnatin Saudiyya take kaddamarwa kan al’ummar kasar, wanda hakan babu wata riba a cikinsa ga kowa.

Daga karshe ya jaddada cewa wajibi ne kasashen Saudiyya da Iran su zauna da juna domin warware matsaloli da dama a yankin gabas ta tsakiya, daga cikin har da yakin kasar Yemen.

3953699

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Najib Amiru
0
0
Hakan zai taimaka sosai amma idan kowa yai da Niya Mai kyau.
captcha