Shafin yada labarai na Abbott Islam ya bayar da rahoton cewa, sakamakon matsanancin sanyi da ake fama da shi a kasar Burtaniya, wata makaranta mallakin musulmi a yankin Blackburn tana bayar da tallafi ga marassa karfi.
Makarantar Zinatul Kur’an da ke yankin na Blackburn, ta kirkiro shirin tallafa wa marassa galihu ne sakamakon yanayin da ake ciki na sanyi da kuma cutar corona da ake fama da ita.
Shugaban makarantar Maulana Farouq Patel ya bayyana cewa, a kowace shekara ana fama da sanyi a lokacin hunturu, amma lokacin na wanann shekara ya banbanta da sauran lokuta, saboda matsalar corona da ake fama da ita.
Ya ci gaba da cewa, daya daga cikin koyarwa irin ta addinin muslunci shi ne taimaka ma mabukaci da duk abin da ya sawaka, domin ya samu sauki daga tsananin da yake ciki, wanda kuma hakan aiki ne na ‘yan adamtaka.
Maulana ya kara da cewa, wannan shiri zai ci gaba da yardar Allah, inda za su rika yin aikin a dukkanin sassa na kasar Burtaniya, domin taimaka ma duk wanda suka ga yana cikin yanayi na bukatar taimako.