IQNA

16:35 - February 19, 2021
Lambar Labari: 3485668
Tehran (IQNA) Rauhani ya kirayi gwamnatin Amurka da ta yi aiki da nauyin da ya rataywa a wuyanta dangane da yarjejeniyar Nukiliya

Shugaban na Kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya kirayi gwamnatin Amurka da ta yi aiki da nauyin da ya rataywa a wuyanta dangane da yarjejeniyar Nukiliya, kuma ta yi aiki da kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231.

Shugaban na kasar Iran ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da wasu sabbin kamfanoni a jiya Alhamis.

Har ila yau shugaban na kasar Iran ya yi ishara da irin matsin labarin da Amurkan take yi wa jamhyuriyar musulunci ta Iran, yana mai nuna fatansa na ganin sabuwar gwmanatin Amurka ta biya Iran fansar asarar da ta haddasa ma ta.

Wani sashe na jawabin shugaban kasar ta Iran ya kuma bayyana cewa; Aiki da doka da yarjeniyoyin kasa da kasa, daya ne daga cikin nauye-nauyen da su ka rataya akan kowace kasa, don haka muna fatan ganin sun yi aiki da dokokin domin samun kyakkyawan yanayi a duniya.

Sabuwar gwamnatin Amurka dai ta nuna cewa a shirye ta koma cikin yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, kuma yanzu haka Amurka na tattauna wannan batu tare da kasashen kungiyar tarayyar turai.

3954818

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: