IQNA

Najeriya: Za A Saka Ranakun Hutu Na Musulunci A Cikin Kalanda A Jihar Oyo

22:19 - February 25, 2021
Lambar Labari: 3485689
Tehran (IQNA) gwamnan jihar Oyo a tarayyar Najeriya ya sanar da cewa za a saka ranakun hutu na musulunci a cikin kalandar jihar.

Shafin jarisar Daily Post ya bayar da rahoton cewa, Seyi Makinde gwamnan jihar Oyo da ke tarayyar Najeriya ya sanar da cewa, za a saka ranakun hutu na musulunci a cikin kalandar jihar.a hukumance.

Makinde ya ce wajbi ne musulmi da wadanda ba musulmi ba su ci gaba da rayuwa da juna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, kuma gwamnatin jihara  cewarsa, ba za ta taba bari a mayar da jihar Oyo wurin tashin hankali da nuna wa wasu 'yan Najeriya bangaranci ba.

Hadin kai tsakanin dukkanin al'ummomin jihar da ma wadanda suka zo suna zaune a  jihar lami lafiya, shi ne abin da zai kawo wa jihar tasu ci gaba, da bunkasar rziki.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, manzon Allha (SAW) ya koyar da musulmi kyawawan dabi'u tare da kyautata mu'amala da kowa, a kan haka, yin koyi da wadannan dabi'u na ma'aiki za su taimaka ma musulmia  duk inda suke wajen zama da kowa cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna.

3956218

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha