IQNA

20:21 - February 26, 2021
Lambar Labari: 3485692
Tehran (IQNA) kungiyar matasa musulmi ta gina wani sabon masallaci a kasar Ghana.

Shafin yada labarai na Modern Ghana ya bayar da rahoton cewa, kungiyar matasa musulmi ta (Association Concerned Muslim Youth) ta kammala ginin masallaci wanda aka bude a yau Juma’a a kasar Ghana.

Wannan masallaci dai baya ga wurin salla, yana da wurare daban-daban da suka hada da bangaren gudanar da tarukan addini, cibiyar kiwon lafiya, da kuma bangaren koyon hardar kur’ani mai tsarki.

Cibiyar Sheikh Mustafa Ibrahim (ICODEHS)da ke daukar nauyin ayyukan alhairi a kasar Ghana, ita ce ta taimaka ma matasan wajen gina wannan katafaren masallaci a yankin arewa maso gabashin kasar Ghana.

 

3956298

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: