IQNA

Haniyya: Gwagwarmaya Ce Kawai Za Ta Hada Kan Al'ummar Falastinu

19:49 - March 01, 2021
Lambar Labari: 3485702
Tehran IQNA, Isma’il Haniyya Shugaban kungiyar Hamas ya gana da jakadun wasu kasashen a birnin Doha na kasar Qatar.

A yammacin jiya shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya gana da jakadun kasashen Rasha, Iran, Turkiya Da Kuma Afirka Ta Kudu a birnin Doha na kasar Qatar, inda aka tattauna batutuwa da dama da suka shafi halin da ake ciki a Falastinu.

Isma’il Haniyya ya bayyanawa jakadun wadannan kasashen matsayar Hamas dangane da ci gaba da ayyukan wuce gona da iri da Isra’ila take yi a cikin yankunan Falastinawa, inda Hamas take ganin cewa daukar matakan kare kai daga bangaren Falastinawa ya zama wajibi.

Baya ga haka kuma ya bayyana musu halin da ake ciki dangane da shirin gudanar da tattaunawa wadda za ta hada dukkanin bangarorin Falastinawa, da kuma batun gudanar da zabuka na Falastinu.

Dangane da halin da ake ciki yankin zirin Gaza kuma ya bayyana cewa har yanzu al’ummar yankin suna cikin matsaloli masu tarin yawa, sakamakon killace yankin da kuma haramta musu abubuwan da suke bukata na rayuwa da Isra’ila ke ci gaba da yi.

3956847

 

 

 

captcha