A cikin wani bayani, ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanar da cewa, babu wata bukatar tattaunawa a halin yanzu tsakanin kasar ta Iran da kuma Amurka gami da kasashen turai kan yarjejeniyar nukiliya.
A cikin wani bayani wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar, ta bayyana cewa; a halin yanzu babu wata bukatar tattaunawa tsakanin kasar ta Iran da kuma Amurka gami da kasashen turai kan yarjejeniyar nukiliya da aka rattaba hannu a kanta.
Bayanin ya ce, wannan yarjejeniya a tsare take, abin da ya rage shi ne yin aiki da abin da ta kunsa, a kan haka duk wata tattaunawa dole ne ta zama a kan yadda za a yi aiki da ita ne, ba yin gyara ko kwaskwarima a cikinta ba.
Kasashen turai uku wato Burtaniya, Faransa da kuma Jamus, sun gabatarwa Iran bukatar gudanar da zama tsakaninsu da ita da kuma Amurka, domin duba wannan yarjejeniya.
Sai a nata bangaren Iran tana ganin babu bukatar hakan, abu na farko da ya kamata a yi shi ne Amurka ta janye dukkanin takunkuman da ta kakaba mata, wanda sun yi hannun riga da yarjejeniyar, sannan idan akwai bukatar tattaunawa, sai a zauna domin sanin yadda ya kamata kowa ya yi aiki da abin da ke kansa.