IQNA

20:17 - March 02, 2021
Lambar Labari: 3485706
Tehran (IQNA) Shugaban majalisar koli ta siyasa a Yemen Muhammad Ali Alhuthi ya bayyana cewa, abin da al’ummar Yemen suke bukata shi ne dakatar da kisan kiyashin a kansu.

Shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar Yemen Muhammad Ali Alhuthi ya bayyana cewa, babban abin da al’ummar Yemen suke bukata da farko shi ne dakatar da kisan kiyashin da Saudiyya da UAE suke yi a kansu.

A zanatwarsa da mamane labarai a birnin san’a fadar mulkin kasar Yemen, Shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar Yemen Muhammad Ali Alhuthi ya jaddada cewa, gudanar da taron kasa da kasa na tattara taimakon kudade ga al’ummar Yemen ba shi ne abun da mutanen Yemen suka fi bukata ba a yanzu, abin da suke bukata shi ne dakatar da ‘yan mamaya daga yi musu kisan kiyashi.

Alhuthi ya ce, wasu daga cikin kasashen duniya suna kokarin bayyana kansu a matsayin kasashen da babu ruwansu, kuma su masu taimako ne ga al’ummar Yemen, amma kuma a lokaci guda su ne suke sayar da makaman da ake kashe al’ummar Yemen da su.

Ya jaddada cewa dole ne a dakatar da makiya al’ummar yemen daga kisan kiyashin da suke yi, tare da kawo karshen killacewar da suke yi wa kasar, sannan a yi maganar taimaka mutane da abubuwan da suke bukata na rayuwa wanda aka haramta musu.

3957051

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: