IQNA

Tsauraran Matakai A Masallacin Haramin Makka Saboda Gabatowar Watan Ramadan

21:42 - March 10, 2021
Lambar Labari: 3485733
Tehran (IQNA) an dauki tsauraran matakai a masallacin haramin Makka mai alfarma saboda gabatowar watan Ramadan

Mahukunta  a kasar Saudiyya sun dauki matakai dangane da yadda taruka da sauran ayyukan ibada na ziyara za su kasance a masallacin haramin Makka a watan Ramadan.

Kafofin yada labaran kasar Saudiyya sun bayar da rahotannin cewa, a yau an yi ganawa ta musamman tsakanin wakilin shugaban cibyar kula da haramomi biyu masu alfarma na Makka da Madina Sa’ad Almuhaimid, da kuma Yusuf Alkhudaid, babban jami’I mai kula harkokin tsaro a dukkanin haramomin biyu masu alfarma.

Ganawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a gudanar da tarukan ziyara da sauran ayyuka na ibada a cikin haramomin Makka mai alfarma a watan Ramadan, musamman ma ganin cewa har yanzu akwai barazanar yaduwar cutar corona.

Majiyoyin suka ce bangarorin biyu sun cimma matsaya kan yadda ziyarar Umrah za ta kasance, da kuma yadda taruka a cikin haramin Makka mai alfarma za su kasance a cikin watan an Ramadan.

Daga ciki har da takaita yawan jama’a kamar yadda aka yi a shekarar bara, sannan kuma za a kara karfafa batun kiyaye ka’idoji na kiwon lafiya, da kuma tsaron lafiya masu ziyara.

Yanzu haka akwai jami’an bayar da agajin gaggawa kimanin 214 da suka shirya tsaf domin gudanar da ayyukansu a tsawon watan Ramadan a haramin mai alfarma, kamar yadda kuma bayar da layukan tarho da za a iya bugawa a duk lokacin da wani abu na gaggawa ya taso da ake bukatar dauki cikin sauri.

3958883

 

 

captcha