IQNA

An Dage Ziyarar Netanyahu Zuwa UAE Saboda Sabani Da Jordan

2:05 - March 12, 2021
Lambar Labari: 3485738
Tehran (IQNA) an dage ziyarar da firayi ministan Isra'ila ya shirya gudanarwa a kasar UAE a yau saboda wani sabani da ya kunno kai tsakanin Isra'iila da Jordan.

Shafin yada labarai na Arab Weekly ya bayar da rahoton cewa, majiyoyin gwamnatin Isra'ila sun sanar da cewa, a yau ofishin Netanyahu ya bayar da sanarwar cewa, an jingine ziyarar da aka shirya cewa zai gudanar a kasar hadaddiyar daular larabawa.

Bayanin ya ce daukar wannan mataki ya zo ne sakamakon sabanin da aka samu tsakanin Isra'ila da Jordan kan ratsa sararin samaniyar Jordan da jirgin Netanyahu zai yi zuwa UAE.

Jordan taki amincewa da hakan, amma a nata bangaren gwamnatin yahudawan ta sanar da cewa, daukar wannan matakin ya zo ne sakamakon hana yarima mai jiran gadon sarautar Jordan ziyartar masallacin Quds da Isar'ila ta yi a jiya Laraba.

A yau ne dai aka tsara cewa Netanyahu zai kai ziyara ta farko a hukumance a kasar hadaddiyar daular larabawa, bayan da ta kulla alaka da Isra'ila a cikin shekarar da ta gabata..

3959102

 

 

captcha