Shafin yanar gizo na gwamnatin Falastinawa ya bayyana cewa, a cikin bayanain da ya zo daga ma’aikatar harkokin wajen Falastinu, Isra’ila tana ci gaba da gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan Falastinawa da ta mamaye.
Bayanin ya ce wannan na zuwa a daidai lokacin da zaben Isra’ila ke karatowa, inda gwamnatin Netanyahu ke son yin amfani da hakan wajen samun kuri’u a zabe mai zuwa.
Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da yadda ginin matsugunnan yahudawan ya karua cikin ‘yan lokutan baya-bayan nan, a daidai lokacin da kasashen duniya da ma majalisar dinkin duniya suke yin kira ga gwamnatin yahudawan da ta dakatar da hakan.
Ita ma a nata bangaren kungiyar tarayyar turai ta fitar da bayanai daban-daban da a ciki take yin gargadi ga gwamnatin yahudawan da ta dakatar da ginin matsugunnan yahudawa a cikin yankunan Falastinawa.
Yanzu haka dai akwai dubban gidajen da Isra’ila take cikin ginawa a matsugunnai daban-daban a cikin yankunan Falastinawa da ta mamaye a gabar yammacin kogin Jordan.