IQNA

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Yi Bayani Kan Matsayin Shahidai

20:21 - March 30, 2021
Lambar Labari: 3485771
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajibcin ƙara ƙaimi wajen kiyaye koyarwar juyin musulunci

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajibcin ƙara ƙaimi wajen karewa da kuma kiyaye koyarwar juyin juya halin Musulunci daga makircin maƙiya.

Jagoran ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a wajen taron shahidai 4000 na lardin Yazd na ƙasar Iran ɗin da aka gudanar a ranar 15 ga watan Maris ɗin nan wanda a yau Talata ofishin Jagoran ya fitar da jawabin.

Jagoran ya ce wajibi ne a kiyaye sakonnin shahidai da kuma ƙarfafa wannan tafarki na su na tsayin daka, yana mai cewa manufar yin hakan ita ce kiyaye juyin juya halin, koyarwar marigayi Imam Khumaini da kuma kawar da baƙar aniyar maƙiya.

Yayin da ya ke magana kan shahidan lardin Yazd ɗin kuwa, Ayatullah Khamenei ya ce wajibi ne a gabatar da fuskokin waɗannan shahidai masu haske ga matasan yanzu don su fahimci irin girman matsayi da kuma sadaukarwar da ‘yan baya suka yi.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da ƙoƙarin da maƙiyan Iran suke ci gaba da yi wajen kawar da matasa daga tafarkin juyin juya halin Musulunci, don haka ya ce bai kamata a bari wannan baƙar aniya ta maƙiyan ta shafi matasan ba.

Daga ƙarshe dai Jagoran ya jinjinawa irin haƙuri da juriya da iyaye, mataye da kuma iyalan shahidan suka nuna kuma suke ci gaba da nunawa sakamakon rashin waɗannan ababen ƙaunar na su.

 

3961762

 

captcha