IQNA

20:26 - March 30, 2021
Lambar Labari: 3485772
Tehran (IQNA) yahudawan sahyuniya nashirin kaddamar da samame a kan masallacin quds mai alfarma da sunan raya idin Haikal Mauhum na yahudawa.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, a cikin wannan makon wasu gungun yahudawan sahyuniya nashirin kaddamar da samame a kan masallacin quds mai alfarma da sunan raya idin Haikal Mauhum na yahudawa.

Wannan gungun yahuudawa masu tsatsauran ra’ayi suna kaddamar da irin wannan smame a kan masallacin quds lokaci zuwa lokaci da sunan suna gudanar da tarukansu na yahudawa.

Gwamnatin yahudawan Isra’ila tana bayar da cikakken tsaro ga yahudawan a duk lokacin da suke shirin kai wannan samame domin keta alfarmar masallacin quds.

Sakamakon irin wannan danyen aiki na yahudawan, al’ummar Falastinu sun sha mika koke ga bangarori na kasa da kasa da kuma majalisar dinkin duniya domin daukar matakai, amma kuma babu wani mataki da ake dauka kan hakan.

 

 

3961540

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mika koke ، bangarori ، mataki ، majalisar dinkin duniya ، tsaro
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: