IQNA

Al’ummar Bahrain Sun Sake Dawowa Kan Tituna Domin Neman Hakkokinsu Da Aka Haramta Musu

20:00 - April 05, 2021
Lambar Labari: 3485785
Tehran (IQNA) al’ummar kasar Bahrain sun sake dawowa kan tituna domin hakkokinsu da masarautar kama karya ta kasar ta harmata musu a matsayinsu na ‘yan kasa.

Mutanen kasar Bahrain suka fitowa kan titunnan biranen kasar don neman sarakunan kasar su saki fursinonin da suke tsare da su a gidajen yari sabodar bullar cutar korona a cikinsu.

Masu zanga-zangar sun bukaci sarakunan Ali Khalifa su sake fursinonin da suke tsare da su a gidajen yarin kasar saboda yadda cutar korona take kara yaduwa cikinsu.

Masu zanga-zangar sun yi allawadai da yadda gwamnatin take boye labarin irin barnan da cutar korona take yi a cikin gidajen yarin kasar.

Kafin haka dai, a ranar Alhamis da ta gabata ce babban malamin addini na kasar Sheikh Isa Qasim ya yi kira ga gwamnatin sarakunan kasar, da su kawo karshen tsare fursinoni a gidajen yarin kasar, don ci gaba da tsaresu tamkar yanke masu hukuncin kissa ne.

Tun shekara ta 2011 ne mutanen kasar Bahrian suke zanga-zangar neman hakkinsu na zaben shuwagabanninsu da kuma bukatar a sauya tsarin mulkin kasar ta yadda mutane zasu zabi shuwagabanninsu da kansu.

 

3962505

 

 

captcha