Shafin Aljumhuriya online ya bayar da rahoton cewa, gwamnan lardin Kafar Alsheikh a kasar Masar ya bayar da sanarwar cewa, gwamnatin lardin za ta shirya gasar kur’ani domin tunawa da babban malamin kur’ani a kasar Masar Sheikh Abul Ainain Shu’aish.
Ya ce wannan gasa za ta fara gudana nea cikin watan Ramadan mai alfarma, kuma tuni aka bude kofar yin rijista ga masu bukatar shiga a shekaru daban-daban.
Ya ce masu karancin shekaru akwai bangaren da aka ware musu idan suna son shiga wannan gasa, kamar yadda masu matsakaitan shekaru ma hakan har zuwa shekara sha uku za su iya yin gasa a bangaren juzu’i na 9,20,30.
Daga shekaru 18 abin da ya yi sama kuma za su iya shiga gasar a dukkanin bangarorinta, da hakan ya hada da tilawa, harda, da kuma sanin kaidojin karatu da hukuncinsa.