IQNA

23:51 - April 16, 2021
Lambar Labari: 3485815
Tehran (IQNA) magoya bayan Harkar Musulunci a Najeriya sun gudanar da jerin gwanon neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky tare da mai dakinsa.

Daruruwan magoya bayan Harkar Musulunci a birnin Abuja na Najeriya sun gudanar da jerin gwanon neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky tare da mai dakinsa malama Zinat Ibrahim

An gudanar da wannan gangami da jerin gwano ne dai a Garki da ke Abuja fadar mulkin Najeriya, domin nuna damuwa kan ci gaba da tsare jagoran Harkar Musulunci da ake a gidan kason Kaduna tare da mai dakinsa.

Masu jerin gwanon sun rika rera taken yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki malmin, musamamn ganin cewa ba shi da isassar lafiya, inda yake bukatar kulawa ta musamman.

Tun bayan kama sheikh Ibrahim Zakzaky a karshen shekara ta 2015 da sojoji suka yi, bayan kisan adadi mai yawa na magoya bayansa a Zariya, har yanzu ana ci gaba da tsare tare da mai dakinsa, ba tare da yanke musu wani hukunci ba.

3964953

تظاهرات شیعیان نیجریه در اعتراض به ادامه حبس غیرقانونی شیخ زکزاکی

تظاهرات شیعیان نیجریه در اعتراض به ادامه حبس غیرقانونی شیخ زکزاکی

تظاهرات شیعیان نیجریه در اعتراض به ادامه حبس غیرقانونی شیخ زکزاکی

تظاهرات شیعیان نیجریه در اعتراض به ادامه حبس غیرقانونی شیخ زکزاکی

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: