IQNA

Azumi Horo Ne Domin Karfafa Ruhi Da Jikin Dan Adam Domin Jurewa Kowane Yanayi Na Rayuwa

23:48 - April 17, 2021
Lambar Labari: 3485818
Tehran (IQNA) wakilin jami’ar Al-mustafa a Pakistan ya bayyana cewa, azumi wani horo ne ga dan adam domin horar da shi kan dukkanin yanayi na rayuwa.

Wakilin jami’ar Al-mustafa a kasar Pakistan Hojjatol Islam Dadsarasht ya bayyana cewa, shi azumi wani horo ne ga dan adam domin horar da shi kan dukkanin yanayi an rayuwa tare da ba shi tarbiya da ladabtarwa.

Malmin ya ce idan aka yi la'akari da dukkanin lamurra da suka shafi sha'anin azumi, tun daga farkon ayar da ta sauka da ke wajabta shi, har zuwa sauran lamurra da suka shafi yadda ake gudanar da shi da kuma hukunce-hukuncensa, za a ga cewa dukkanin lamarin ya doru ne a kan tarbiyar dam.

Wannan tarbiya kuwa manufar guda daya ce, ita ce kai dan adam zuwa mataki na taqwa wato tsoron Allah, domin da tsoron Allah ne dam adam yake kai wa ga mataki na kololowa na kamala.

3963952

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha