IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Farmakin Yahudawa A Kan Musulmi A Birnin Quds

23:41 - April 24, 2021
Lambar Labari: 3485842
Tehran (IQNA) kungiyar Hizbullah ta yi Allawadai da farmakin yahudawa a kan musulmi a birnin Quds.

Kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta fitar da bayani da ke nuna cikakken goyon bayan kungiyar ga al’ummar Falastinu, dangane da cin zarafin da suke fuskanta daga yahudawan Isra’ila.

Bayanin ya ce, kungiyar Hizbullah tana yin tir da Allawadai da kakkausar murya, dangane da cin zarafin da yahudawa suke yi wa musulmin Falastinu, kamar yadda kuma ta yi Allawadai da farmakin da yahudawan suka kai kan masallata a jiya a birnin Quds a lokacin sallar Juma’a.

Bayanin ya ci gaba da cewa, abin da yake faruwa ta’addanci ne tsararre, wanda ke nufin ci gaba da murkushe al’ummar Falastinu tare da mayar da su saniyar ware a cikin kasarsu, wanda hakan kuma yana faruwa a kan idanun dukkanin al’ummomin duniya.

Daga karshe kungiyar bayan ta kara nuna cikakken goyon bayanta ga al’ummar falastinu, ta kuma kirayi al’ummomin duniya musamman masu lamiri daga cikinsu, da su sauke nauyin da ya rataya a kansu, wajen bayar da kariya ga al’ummar Falastinu.

 

3966634

 

captcha