IQNA

Najeriya: Sojoji Sun Ce Sun Dakile Wani Yunkurin Harin Boko Haram A Jihar Yobe

23:46 - April 24, 2021
Lambar Labari: 3485843
Tehran (IQNA) sojojin Najeriya sun ce sun dakile wani yunkurin da Boko Haram ta yi na kai hari a garin Geidan da ke jihar Yobe.

Shafin Nig24 News ya bayar da rahoton cewa, sojojin Najeriya sun ce sun dakile wani yunkurin mayakan Boko Haram na kai hari a garin Geidan da ke jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran PRNigeria ya bayar da rahoton cewa, mayakan Boko Haram A cikin motoci 10 sun tunkari garin Geidam da ke cikin jihar Yobe arewa maso gabashin Najeriya, amma sojoji sun yi amfani da jiragen yaki wajen tarwatsa su.

Bisa ga bayanin sojojin, mayakan Boko Haram sun kudiri aniyar kai harin a jiya Juma'a gab da lokacin da ake shirin yin buda baki.

Haka nan kuma bayanin sojojin ya kara da cewa, wasu daga cikin mayakan Boko Haram da suka fahimci halin da ake ciki sun tsere kafin kai musu hari, yayin da kuma aka rutsa da wasu aka kashe wani adadi daga cikinsu.

 

3966780

 

captcha