IQNA

Kwamitin Tsaron MDD Ya Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Wuraren Da Ake Fama Da Rikici

15:02 - April 29, 2021
Lambar Labari: 3485859
Tehran (IQNA) Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya fitar da wani kudiri da ke yin Allawadai da kisan fararen hula a duk wani wuri da ake rikici a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar a jiya, fitar da wani kudiri da ke yin Allawadai da kisan fararen hula ko kai hare-hare a kansu a duk wani wuri da ake fama da rikici a duniya, tare da kiran dukkanin bangarori da suke rikici da juna da su kiyaye rayukan fararen hula, kuma su guji kai hare-hare a kan yankunansu.

Dukkanin mambobin kwamitin tsaron 15 ne suka amince da wannan kudiri mai lamba 2573, wanda baya ga yin Allawadai da kisan fararen hula a lokutan rikici, ya kuma bukaci bangarorin da suke rikici a ko'ina ne a duniya, da su bayar da damar kai agajin gaggawa ga fararen hula.

Haka nan kuma kudirin ya ya jaddada wajabcin isar da kayayyakin kiwon lafiya da hakan ya hada da rigafin cutar corona ga fararen hula a dukkanin yankunan da ake fama da rikici a duniya.

Kwamitin tsaron ya bayyana yin duk wani abin da ya saba wa hakan yana a matsayin tafka laifukan yaki ne, wanda kuma akwai hukunci mai tsanani da kotun duniya ta yi tanadi a kan hakan.

 

 

3967852

 

 

 

captcha