IQNA

‘Yan Jarida Da Ma’aikatan Yada Labarai 337 Ne Suka Rasa Rayukansu Cikin Shekaru 6 A Yemen

21:41 - May 05, 2021
Lambar Labari: 3485879
Tehran (IQNA) ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai 337 ne suka rasa rayukansu a Yemen a cikin shekaru 6 sakamakon hare-haren Saudiyya.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, kungiyar ‘yan jarida ta kasar Yemen ta fitar da wani rahoto da ke cewa, a cikin shekaru 6 da Saudiyya ta kwashe tana luguden wuta a kan al’ummar kasar Yemen, ‘yan jarida da ma’aikata  abangaren yada labarai 337 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren na Saudiyya da UAE.

Rahoton ya ce, 47 daga cikinsu an kashe su ne sakamakon hare-haren da jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar a kan gidajensu, ko kuma a ofisoshinsu a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Sannan kuma rahoton ya kara da cewa, an kashe 290 daga cikinsu ne a fagen daga, a lokacin da suke gudanar da ayyukan bayar da rahotanni da sauran ayyukan da suka shafi bangaren yada labarai daga fagen daga a kasar ta Yemen.

Yanzu haka dai cibiyoyin yada labarai da suka hada da wadanda suke karkashin ma’aikatar yada labarai ta kasar Yemen guda 23 ne Saudiyya ta rusa baki daya, yayin da kuma ta rusa gidajen rediyo guda 30 a kasar ta hanyar kai musu hari da jiragen yaki.

3969269

 

 

 

captcha