IQNA

Sayyid Nasrullah: Taimakon Al'ummar Falastinu Nauyi Ne A Kan Dukkanin Musulmi

18:21 - May 06, 2021
1
Lambar Labari: 3485882
Tehran (IQNA) Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, taimakon al'ummar Falastinu da kuma 'yantar da masallacin Quds daga mamayar yahudawa nauyi ne da ya rataya kan dukkanin musulmi.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasarallah ya bayyana cewa; yahudawan Isar’ila da kansu sun san cewa makomarsu a yankin yammacin Asia ita ce rushewa.
 
Nasarallah yana fadar haka ne a jiya Larana a cikin wani shiri da ake kira Mimbari a tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon.
 
Shugaban kungiyar ta Hizbullah yana magana ne dangane da zagayowar ranar Quds ta duniya wacce za ta kasance gobe 7 ga watan Mayu, wato jumma’a na kasar na watan Ramalana kamar yadda Imam Khomaini (q) wanda ya kafa jumhuriyar Musulunci ta Iran ya ayyana.
 
Sayyeed ya kara da cewa alamun faduwar da kuma wargajewar haramtacciyar kasar Isra’la sun bayyana tare da faduwar ‘Yarjejeniyar karni’ da kuma gwamnatin Donald Trump na kasar Amurka.
 
Ya ce a halin yanzu kasashe da kungiyoyi masu gwagwarmaya ne zasu ayyana makomar yankun kudancin Asia. Sannan sajewar da wasu shuwagabannin kasashen larabawa suka yi da haramtaccikar kasar ba abinda ya kara mana sai kara tabbata a kan goyon bayan al-ummar Falasdinu a gwagwarmayan da suke yi da yahdawan sahyuniya ‘yan ammaya.
 
Har’ila wannan wannan ya kara nauyin da ke kammu na ganin cewa an ‘yentar da masallacin Quds.
 
Daga babban sakataren na kungiyar Hizbulla ya bayyana cewa; musulmi a ko ina suke, duk tare da matsalolin cutar Korona da ake fama da ita, su nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu ta duk wata hanya da ta sawaka a gare su.
 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Mukhtar usman
1
0
ALLAH YABAMA MUSULMI SA.A DUK INDA YAKE
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :