IQNA

Taron Addu'a Ga 'Yan Mata Tamanin Da Suka Rasa Rayukansu A Harin Ta'addanci A Afghanistan

23:45 - May 11, 2021
Lambar Labari: 3485905
Tehran (IQNA) wasu matasa da suka hada da 'yan jami'a a birnin Tehran sun gudanar da taron addu'a ga 'yan matan da suka rasa rayukansu a kasar Afghanistan.

A rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, a yammacin yau Talata, wasu matasa da suka hada da 'yan jami'a a birnin Tehran sun gudanar da taron addu'a ga 'yan matan da suka rasa rayukansu a kasar Afghanistan, wanda aka gudanar a gaban ofishin jakadancin Afghanistan da ke Tehran.

A yayin taron dai an gabatar da bayani na nuna alhini ga ofishin jakadancin Afghanistan kan abin da ya faru, tare da yin Allawadai da haka.

Sannan kuma mahalarta wurin sun jaddada cikakken goyon bayansu ga al'ummar kasar Afghanistan wajen fuskantar 'yan ta'adda masu gurbatacciyar akida ta kafirta musulmi.

Harin ta'addancin da aka kai kan makarantar 'yan mata a kasar Afghanistan ya fuskanci kakkausar suka da martani daga ko'ina cikin fadin duniya, harin da kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh mai dauke da akidar salafiyya jihadiyya ta dauki nauyin kai wa, yayin da kungiyar Taliban ta nisanta kanta da wannan hari.

 

3970797

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yau Talata ، kasar Afghanistan ، matasa ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :