IQNA

Shugaban Majalisar Dokokin Iran Ya ce; Al'ummar Musulmi Na Duniya Suna Tare Da Al'ummar Falastinu

23:39 - May 12, 2021
Lambar Labari: 3485907
Tehran (IQNA) Shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa, al’ummar musulmi za su ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Falastinu.

A lokacin bude zaman majalisar dokokin kasar Iran a jiya Talata, shugaban majalisar Iran Muhammad Qalibaf ya bayyana cewa, yahudawan Isra’ila suna cin karensu babu babbaka a kan wurare masu tsarki na al’ummar msuulmi, tare da zubar da jinin al’ummar Falastinu a kan idanun al’ummomin duniya, amma masu da’awar kare hakkin ‘yan adam ko demokradiyya sun yi shiru da bakunansu.

Ya ce ko shakka babu, Allah yana tare da al’ummar falastinu, kuma musulmi masu lamiri a duk inda suke a duniya suna tare da ‘yan uwansu Falastinawa da ake zalunta, inda ya ce wajibi ne a kan dukkanin musulmi su bayar ad dukkanin guunmawar da za su iya, domin takawa Isra’ila burki, kan kisan kiyashin da take yi a kan al’ummar Falastinu.

A daya bangaren kuma Muhammad Qalibaf ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta’adancin da kungiyar Daesh ta kai kan makarantar ‘yan mata a birnin Kabul na kasar Afghanistan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dalibai mata sama da hamsin, inda ya ce wannan ita ce akidar ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi a duk inda suke, alhali abbu abin da ya hada ta’addancinsu da jihadi ko kuma addinin muslunci.

 

3970751

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha