IQNA

Yadda Aka Gudanar Da Sallar Idin Karamar Salla A Masallacin Aqsa

Tehran (IQNA) duk da irin tsauraran matakan tsaro da Isra'ila ta dauka dubban musulmi sun gudanar da sallar idi a cikin masallacin Quds.

Musulmi kimanin dubu 100 ne suka gudanar da sallar idi a cikin masallacin Quds mai alfarma, duk da irin tsauraran matakan tsaro da Isra'ila ta dauka domin hana su isa masallacin.