IQNA

Wani Babban Kwamandan Dakarun Jihadul Islami Ya Yi Shahada A Gaza

22:49 - May 17, 2021
1
Lambar Labari: 3485925
Tehran (IQNA) wani babban kwamandan dakarun kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul Islami ya yi shahada sakamakon harin Isra'ila a Gaza a yau Litinin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na quds net cewa, a yau Litinin wani babban kwamandan dakarun kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul Islami ya yi shahada sakamakon harin Isra'ila a Gaza.

A cikin bayanin da kungiyar ta fitar ta sanar da cewa, babban gwarzo jarumi Abu Ubaidah ya yi shahada a yau, bayan da jiragen yakin Isra'ila suka kai masa hari a lokacin da yake tafiya a cikin motarsa a yau a garin Gaza.

Bayanin ya ce, wanann bawan Allah yana daga cikin wadanda suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen gwagwarmaya da mamayar Isra'ila a kan yankunan Falastinawa, kuma a yau ya yi shahada a kan tafarkinsa na yaki da makiya Allah da annabawan Allah masu kisan mata da kananan yara.

Ita ma a nata bangaren kungiyar Hamas ta fitar da bayani, inda ta bayyana shahahadar Abu Ubaidah da cewa babban rashi ne ga dukkanin al'ummar falastinu, musamman masu yaki da mamayar Isra'ila.

Sauran kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa daban-daban sun fitar da bayanai kan shahadarsa, inda suke kara jaddaa cewa za su ci gaba da gwagwarmaya a kan tafarkin da ya yi shahada har sai an kawo karshen mamayar makiya Allah a kan kasar Falastinu.

 

3972127

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Mukhtar usman
0
0
ALLAH YAJIKAN MUSULMI
captcha