IQNA

Hizbullah Ta Aike Da Sakon Taya Murnar Nasara Ga Al'ummar Falastinu

20:13 - May 21, 2021
Lambar Labari: 3485935
Tehran (IQNA) kungiyar Hizbullah ta aike da sakon taya murnar samun nasara ga al'ummar Falastinu musammnan zirin Gaza.

A cikin bayanin da kungiyar Hizbullah ta fitar a yau, ta bayyana cewa tana taya dukkanin al'ummar Falastinu musamman kungiyoyin gwagwarmaya kan nuna jarunta da tsayin daka da suka yi a gaban yahudawan sahyuniya.

Bayanin ya ce, gwagwarmayar al'ummar Falastinu ne ta tilasta Isra'ila amimcewa da dakatar da bude wuta, domin kuwa martanin da ta fuskanta ya zo mata da ban mamaki, ta yadda ya tilasta miliyoyin yahudawa boyewa a ramukan karkashin kasa.

Daga karshe bayanin na Hizbullah ya ce, abin da ya faru ya kara fallasa karyar da Isra'ila ke yi kan karfin sojinta, inda baya ga kisan mata da kananan yara da fararen hula da rushe gidajen jama'a babu abin da suka yi, domin kuwa ba su iya fuskantar mayakan kungiyoyin gwagwarmaya gaba da gaba, kamar yadda hakan ya kunyata wasu kasashen larabawa masu zaton cewa za su samu tsaro idan suka kulla alaka da Isra'ila.

3972833

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasashen larabawa ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha