Babban Sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, ya gargadi Isra'ila da cewa duk wani wuce gona da iri kan wurare masu tsarki a birnin Kudus da ta mamaye zai haifar da yakin da zai wargaza gwamnatin Tel Aviv.
Sayyed Hassan Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin ranar Talata, wanda shi ne jawabinsa na farko bayan nasarar da kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa suka samu kan Isra’ila yayin rikicin baya baya nan.
Nasrallah ya ce "Gaza ta ba wa abokan gaba mamaki kwarai da gaske," duba da yadda kungiyoyin Falasdinawa sukayi tsayin daka na kare yankunansu da wurare masu tsarki musamman masallacin Kudus.
Nasrallah ya jinjinawa "tsayin daka" na kungiyoyin gwagwarmayar na Falasdinawa, ya kuma ce dole ne jami'an Isra'ila da sojojinta su sake nazari, kan yadda zasu tinkari Zirin na Gaza nan gaba.
"Abin da Gaza ta yi abun tarihi ne, kuma ya kamata a darajanta shi sosai, "in ji shugaban kungiyar ta Hizbullah.
Nasrallah ya gargadi gwamnatin Isra'ila ta kwana da sanin cewa "keta alfarmar Masallacin Kudus da wurare masu tsarki ba zai tsaya a kan iyakokin Gaza ba, zai iya haifar da yakin a yankin wanda kuma daga karshe zai wargaza Isra'ila."
Sayyid Nasrallah ya jaddada cewa, dukkanin kungiyoyin gwagwarmaya a yankin gabas ta tsakiya kansu hade yake, kuma suna yin aiki tare da juna a bangarori daban-daban domin tunkarar hadarin da ke fuskantar al’ummar yankin da ma sauran musulmi.