IQNA

Majalisar Dinkin Duniya: Hare-Haren Isra’ila Kan Gaza Na Iya Zama Laifukan Yaki

23:46 - May 27, 2021
Lambar Labari: 3485955
Tehran (IQNA) Rahoton majalisar dinkin duniya ya ce hare-haren Isra’ila kan Gaza na iya zama laifukan yaki.

Babbar kwamishiniyar hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa akwai yiyuwar a dauki kisan kiyashin da Isar’ila ta aikata a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, a matsayin laifin yaki, wanda za’a gurfanar da ita a gaban kotun kasa da kasa ta hunkunta irin wadannan laifuffuka.

Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Michelle Bachelet tana fadar haka a safiyar yau Alhamis, a taron da ta yi don sauraron karar da kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta gabatar wa hukumarta kan yakin kwanaki 11 wanda HKI ta kaiwa mutanen Gaza.

Michelle Bachelet ta kara da cewa a zahiri basu ga ‘yan bindiga wadanda Isra’ila ta ce su take kaiwa hare-hare a yankin Gaza ba, sun dai ga fararen hula suna mutuwa saboda hare-haren jiragen yakin Isra’ila.

Bachelet ta ce, bisa kididdiga ta majalisar dinkin duniya, Isra’ila ta kashe falastinawa 242 a hare-harenta a kan yankin Gaza da suka hada da kananan yara 63, tare da jikkata wasu dubbai.

Sannan kuma a yankunan gabar yammacin kogin Jordan, Isra’ila ta kashe falastinawa 28 da suka hada da kananan yara 5, da kuma jikkata wasu da dama.

3974081

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kashe falastinawa
captcha