IQNA

Daruruwan Mutanen Canada Da Firayi Ministan Kasar Suna Juyayin Kashe Musulmi Da Aka Yi

23:52 - June 09, 2021
Lambar Labari: 3485995
Tehran (IQNA) daruruwan mutanen kasar Canada da suka hada da firayi ministan kasar sun taru a wuri guda domin juyayin kisan musulmi da aka yi a kasar.

Tashar CBC ta bayar da rahoton cewa,

Tehran (IQNA) daruruwan mutanen kasar Canada da suka hada da firayi ministan kasar sun taru a wuri guda a dandalin Elgin da ke birnin Ottawa, domin juyayin kisan musulmi da aka yi a kasar, wanda ya daga hankulan kowa a kasar.

A wurin taron musulmi da wadanda ba musulmi sun halarta, inda aka yi juyayi kan abin da ya faru, kamar yadda aka saka furanni a matsayin alamar nuna kauna ga mamatan.

Haka nan kuma shugabar kungiyar mata musulmi a jihar ottawa ta gabatar da jawabi a wurin, inda ta bayyana cewa abin da ya faru abin bakin ciki ne da takaici.

Ta kuma bayyana cewa ya kamata hakan ya zama abin daukar darasi ta yadda za a fuskanci halayen mutane masu tsananin kiyayya da musulmi, ta yadda suke halasta ma kansu ta'addanci da kisan musulmi ba tare da wani fargaba ba.

Bayan faruwar kisan musulmi hudu dukkaninsu iyalan gida guda da wani matashi ya yi da motarsa a ranar Talata da ta gabata, firayi ministan kasar Canada Justin Tredeau ya fitar da bayani, inda ya ce nuna kyama ga musulmi a cikin kasar Canada ba ya da wurin zama , kuma za su shiga kafar wando daya da masu wannan akida ta kin jinin musulmi.

 
 

3976392

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Canada daruruwa musulmi kisa
captcha