A lokacin da yake hudubar Juma'a a jiya, Mukhtar Ali Juma'a minista mai kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa, ta'addanci da barna suna rusa kowace irin al'umma a duniya.
Ya ce ta'addanci da dukkanin nau'oinsa mummunan aiki ne wanda yake kawo cikas da tsaiko a cikin lamurran rayuwa baki daya.
Ya ci gaba da cewa, barna kuwa za ta iya hada abubuwa da yawa, daga cikin akwai cin hanci da rashawa a tsakanin jama'a, barnata dukiyar gwamnati wadda hakki ne na jama'a.
Baya ga haka kuma zalunci tsakanin a'umma, cuta da zamba cikin aminci da ha'inci a cikin lamurran jama'a, dukkanin wadannan nau'oi ne na barna wadanda suke rusa al'umma, da suke cire albarka a cikin rayuwar al'umma.