IQNA

An Yi Janazar Dakarun Hashd Al-Shaabi Su Hudu Da Amurka Ta Kashe A Iraki

22:21 - June 29, 2021
Lambar Labari: 3486062
Tehran (IQNA)an yi jana’izar mayakan rundinar sa kai ta Hashd al-shaabi da Amurka ta kashe a wani hari a kasar Iraki kan iyaka da Siriya.

Rahotanni daga Iraki na cewa an yi jana’izar A Bagadaza babban birnin kasar ta Iraki, inda dubban mayakan kungiyar suka yi fareti gaban ma’abotansu.

Masu faretin na kiran ‘’ mutuwa ga Amurka, da kuma kiran daukar fansa kan mutuwar shahidansu’’

Ana ci gaba dai da nuna damuwa a kasar ta Iraki, bisa la'akari da yadda mayakan ke ci gaba da kiran daukar fansa kan harin na Amurka, ta hanyar kai wa dakarun Amurka a kasar hari.

Idan dai ana tune irin wannan yanayin shi ne ya kai har ga aukawa ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza, a watan Disamban shekarar 2019, wanda daga bisani Amurka ta dau fansa ya hanyar kisan Janar Qassim Sulaimani na Iran, lamarin da kuma daga bisani ya so tayar da wani sabon yaki a yankin.

A halin da ake ciki dai Firaministan Iraki Mustafa al-Kazimi, na ci gaba da kiran a kai zuwaciya nesa, yayin da ya danganta harin na Amurka da keta hurimin kasar.

 

 

 

captcha