A jiya ne sabon ministan harkokin Wajen Isra’ila, Yair Lapid ya jagoranci bude ofishin jakadancin Isra’ilar a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan sahyuniya Lapid, shi ne wani ministan Isra’ila na farko da ya kai ziyarar aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa, kusan watanni biyar bayan kulla danganta tsakanin bangarorin biyu.
Jirgin na Lapid ya bi ta sararin samaniyar kasar Saudiyya ne, wacce a bara ta bude sararin samaniyarta ga jiragen yahudawan Isra’ila.
Ziyarar dai na zuwa ne makonni kadan bayan munanan hare-haren Isra’ila a kan al’ummar falastinawa mazauna yankin zirin Gaza, wadanda suka yi sanadiyar shahadar falastinawa masu yawa, da suka hada da mata da kananan yara da tsoffi.