IQNA

Kasar Afirka Wadda Taken Kasar Ke Kunshe Da Ayar Kur'ani Mai Tsarki

22:43 - July 10, 2021
Lambar Labari: 3486092
Tehran (IQNA) kasar mauritaniya kasar da ke yammacin nahiyar Afirka ce kasar da takenta yake kunshe da ayar kur'ani mai tsarki.

Shafin yada labarai na alsaa.ne ya bayar da rahoton cewa, da dama daga cikin mutane ba su san cewa taken kasar Mauritaniya kunshe yake da ayar kur'ani ba.

Haka nan kuma dukkanin taken an tsara shi a cikin baitoci da kuma kafiya a karshen kowane baiti, wanda a cikin baitukan ne aka saka aya ta 22 daga cikin surat kahafi.

Tun a cikin shekara ta 1960 ne aka amince da saka wannan aya a cikin taken kasar mauritaniya, amma sai a cikin shekara ta 2017 ne da aka sake fasalin taken, aka saka wannan aya mai tsarki.

Kasar Mauritaniya dai na daga yammacin nahiyar Afirka ne, kuma akasarin mutanen kasar larabawa ne, kamar yadda harshen kasar larabci ne a hukumance.

 

3982990

 

 

captcha