Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a yau mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da janye dokar hana bude wuraren kasuwanci a lokacin salloli biyar na kowace rana a fadin kasar.
Rahoton ya ce, hukumomin sun sun sanar da cewa, daga yanzu masu shaguna za su iya barin shagunansu a bude a lokacin salloli biyar na wajibi, sabanin lokutan baya inda bisa doka dole ne akalla mintuna talatin na lokacin kowace salla, shaguna da wuraren kasuwanci su zama a rufe.
Mahuntan na kasar Saudiyya dai sun bayyana wannan mataki da cewa, zai taimaka wajen rage yawan cukoso a kasuwanni da kuma shaguna da jama'a suke yin sayayya, da kuma rage jama'a da suke kan jiran masu shaguna a lokacin salla, kamar yadda kuma a cewar bayanin, zai taiamaka wajen rage kamuwar cutar corona.
Sai a nata bangaren jaridar Ukaz mallakin gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa, janye dokar rufe shaguna da wuraren kasuwanci a kasar, yana daga cikin sauye-sauyen da Muhammad Bin Salman yarima mai jiran gadin sarautar kasar ya zo da su.