IQNA

Hukumar Judo Ta Duniya Ta Dakatar Dan Wasan Aljeriya Saboda Yaki Yin Wasa Da Bayahuden Isra'ila

23:45 - July 24, 2021
Lambar Labari: 3486135
Tehran (IQNA) Hukumar wasannin Judo ta duniya ta dakatar da dan wasan Judo na kasar Aljeriya da ya janye saboda kada ya yi wasa da bayahuden Isr’ila a wasannin Olympics na Japan.

A rahoton da tashar Aljazeera ta bayar, a cikin bayanin da hukumar wasannin Judo ta duniya ta dakatar da dan wasan Judo na kasar Aljeriya Fathi Nurain, tare da mai horar da shi zuwa wani lokaci a nan gaba, saboda janyewa da ya yi daga gasar Olympics, domin kada ya yi wasa da bayahuden Isr’ila a wannan gasa.

Rahoton ya ce, bayan daukar wanan mataki, Fathi ya yi hira da manema labarai, inda ya jaddada cewa matsayinsa dagane da Falastinu tabbatacce ne, zai fifita goyon bayan al’ummar Falastinua akn duk wani abin da zai samu daga wasan Judo, saboda haka ya san Allah ba zai bar shi ba, zai musaya masa da mafi alhairi kan hakan.

Matakin na Nurain dai ya zo ne bayan kada kuri'ar da aka yi a bangaren wasan Judo, inda zai kara da Muhamamd Abdulrasul dan kasar Sudan a zagayen farko, idan har ya samu nasar, to karawa ta gaba zai hadu da bayahuden Isra'ila ne.

Ganin haka a nan take Fathi Nurain ya sanar da cewa ya janye daga gasar baki daya, saboda ba zai hadu da bayuhuden Isra'ila ba.

Wanda yake horar da 'yan wasan Judo a kasar Aljeriya Ammar Bin Yakhluf ya bayyana cewa, Fathi Nurain ya janye ne domin nuna rashin amincewa da zaluncin da Isra'ila take yi a kan al'ummar Falastinu, tare da haramta musu hakkokinsu a cikin kasarsu.

Haka nan kuma ya jaddada cewa daukar duk wani mataki ba zai iya canja matsayar da Nurain ya dauka dangane da wannan wasa ba, domin kuwa batu ne na imani.

 

3986083

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Fathi Nurain imani
captcha