IQNA

22:34 - July 25, 2021
Lambar Labari: 3486138
Tehran (IQNA) duk da yakin da kawancen Saudiyya ke kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen makarantun kur'ani ba su dakatar da koyarwa ba.

Shafin yada labarai na Alahad ya bayar da rahoton cewa, duk da yakin da kawancen Saudiyya ke kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen makarantun kur'ani ba su dakatar da koyarwa ba a fadin kasar.

Rahoton ya ce yanzu haka akwai sabbin tsare-tsare na makarantun kur'ani wadanda aka fara aiwatarwa domin amfanin yara dalibai a makarantun na kur'ani a birnin san'a da wasu birane na kasar Yemen.

Daga cikin shirye-shirye har da samar da tsarin koyarwa ta hanyoyi na nesa ta yadda yara za su iya koyon wasu abubuwan daga gida ba tare da halartar ajujuwa ba, ta yadda za su iya yin amfani da manhajojin karatu da ake sakawa a wayoyin salula.

Baya ga haka kuma akwai tsarin koyar da karatun da hukunce-hukuncensa, da kuma koyar da hardar kur'ani mai tsarki cikin sauki yara.

 

3985945

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: koyar da harda ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: