IQNA

22:47 - July 25, 2021
Lambar Labari: 3486139
Tehran (IQNA) Hukumomi a Saudiyya, sun ce za a bude Umra ga ‘yan kasashen waje a farkon watan Muharam.

Shafin hukumar da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain, ya rawaito a shafinsa na Tuwita cewa za’a fara Umra a ranar 10 ga watan Agusta mai zuwa wanda wata killa zata fado da 1 ga watan Muharam na shekarar hijira ta 1443 mai shirin kamawa.

Matakin dai na zuwa kwanaki kadan bayan kammala aikin hajjin bana, wanda karo na biyu a jere mahajatta daga kasashen waje basu samu halarta ba sakamakon annobar korona.

Hukumomin Saudiyya sun takaita aikin hajjin ne ga mutum 60,000 mazauna kasar, domin hana yaduwar sabbin nau’ukkan cutar corona.

 

3986156

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Umra ، saudiyya ، aikin hajji ، cutar corona ، a jere
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: