IQNA

22:53 - July 27, 2021
Lambar Labari: 3486146
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Lebanon Michael Aoun ya umarci Najib Miqati da ya kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Tashar Aljazeerah ta bayar da rahoton cewa, a Litinin Shugaban kasar Lebanon Michael Aoun ya umarci Najib Miqati tsohon firayi ministan kasar, da ya kafa sabuwar majalisar ministoci a kasar.

Wannan yana zuwa ne dai bayan da Saad Hariri ya kasa kafa gwamnati ne bayan shudewar watanni 9 a jere, inda daga karshe ya mika sunayen wasu ministoci da ya zaba, wanda hakan bai samu amincewar wasu da dama daga cikin bangarorin siyasar kasar ba, daga karshe ya sanar da cewa ya neman uzuri, kuma a jiye muamin nasa.

Shugaba Aoun ya kirayi zaman majalisa a yau domin ta fitar da sunan mutum guda wanda zai kafa gwamnati, inda ‘yan majalisa 73 suka amince da Najib Miqati, 42 kuma ba su ambaci sunan kowa ba, sai kuma 3 daga cikin ‘yan majalisar ba su halarci zaman na yau ba.

 

 

3986598

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: