IQNA

Azhar Ta Sanar Da Cikakken Goyon Bayanta Ga Iraki Wajen Yaki Da Ta'addanci

20:45 - August 01, 2021
Lambar Labari: 3486158
Tehran (IQNA) cibiyar ilimi ta Azhar ta sanar da cikakken goyon bayanta ga gwamnatin kasar iraki wajen yaki da ta'adanci.

Shafin yada labarai na Mawazin ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar cibiyar ilimi ta Azhar ta sanar da cikakken goyon bayanta ga gwamnatin kasar iraki wajen yaki da ta'adanci a fadin kasar.

Bayanin na Azhar ya ce, masu kaddamar da hare-haren ta'addanci da sunan addini, abin da suke yi ba shi da wata alaka da addinin mulsunci, kamar yadda kuma ya yi hannun riga da 'yan adamtaka, a kan haka gwamnatin Iraki hakki ne a kanta ta yaki wadannan masharranta.

Haka nan kuma Azhar ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta'addancin da aka kai kan lardin Salahuddin a ranar Asabar da ta gabata, inda jami'an tsaro da fararen hula suka rasa rayukansu, hare-haren da 'yan ta'addan takfir na Daesh suka dauki nauyin kaddamar ad su.

A cikin kwanakin nan dai kungiyar daesh ta fara dawowa da hare-harenta na ta'addanci a kasar Iraki, wanda kuma hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Iraki suke matsa lamba kan Aurka da ta fitar ad sojojinta daga kasar, yayin da kuma wasu bayanai na tsaro daga bangarori daban-daban a kasar ta Iraki suke yin ishara da cewa, Amurka tana da kyakkyawar alaka da kungiyar ta Daesh a cikin kasar ta Iraki.

 

3987661

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: cibiyar ، fitar ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha