IQNA

A Ranar Talata Mai Zuwa Za A Rantsar Da Zababben Shugaban kasar Iran

22:58 - August 01, 2021
Lambar Labari: 3486160
Tehran (IQNA) a jibi Talata Jagoran juyin juya halin Musulunci zai miƙa wa zaɓɓaɓen shugaban kasa takardar amincewarsa da zaɓan da aka yi masa a matsayin shugaban ƙasa.

A wata sanarwa da ofishin Jagoran ya fitar a yau Lahadi ya ce a bikin da za a gudanar a Husainiyar Imam Khumaini da ke gidan Jagoran, Ayatullah Khamenei zai ba wa Sayyid Ra’isi takardar amincewarsa da zaɓan da aka masa a matsayin shugaban ƙasar Iran.

Sanarwar ta ƙara da cewa a yayin bikin wanda zai samu halartar wasu daga cikin manyan jami’an ƙasar, ministan cikin gida na Iran ɗin zai gabatar da rahoto kan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuni, daga nan kuma za a karanta abin da takardar kama aikin ta ƙumsa sai kuma jawabin da sabon shugaban da kuma Jagoran za su yi.

Bikin miƙa takardar amincewa da shugabancin dai shi ne mafarin kama aiki duk wani shugaban ƙasa da aka zaɓa a Iran.

A ranar Alhamis, kwanaki biyu bayan wannan bikin ne dai ake sa ran Sayyid Ibrahim Ra’isin zai gudanar da rantsuwar kama aiki a hukumance a gaban ‘yan majalisar dokoki na Iran ɗin wanda hakan ke nufin kawo ƙarshen gwamnati mai ci yanzu da kuma fara aikin sabuwar gwamnatin.

 

 

3987738

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha