IQNA

Saudiyya Ta Haramta Wa 'Yan Kasashe 33 Gudanar Da Ayyukan Ibadar Umrah

23:57 - August 09, 2021
Lambar Labari: 3486185
Tehran (IQNA) Gwamnatin Saudiyya ta haramta wa 'yan kasashe 33 gudanar da ayyukan ibadar Umrah

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Gwamnatin Saudiyya ta haramta wa 'yan kasashe 33 gudanar da ayyukan ibadar Umrah saboda dalilai na kiwon lafiya.

Rahoton ya ce, mai yiwuwa gwamnatin kasar ta Saudiyya ta fitar da jerin sunayen a hukumance ga kafofin yada labarai.

Sai dai tuni shafin almisrawi ya fitar da sunayen wasu daga cikin wadannan kasashe, da suka hada da Amurka, Masar, Afirka ta kudu, Italiya, Faransa, Switzerland, Ingila, Swden, Jamus, Argentina, Brazil, Japan, China, Turkiya, India, Indonesia, Pakistan , Iran, Liberia, Gunea Bissau, Portugal, Armenia, Lebanon, Hadadiyar Daular Larabawa da sauransu.

A nata bangaren ma'aikatar kula da harkokin aikin hajji da Umrah ta sanar da cewa, ta sanar da sauran kasashe cewa an bude kofar ayyukan umrah, amma dukkanin mutanen da za a iya karba daga kasashen da amince zuwansu ba zai wuce mutane dubu 60 ba a baki daya.

A daya bangaren kuma a karon farko an nada mata guda biyu ga shugaban hukumar da ke kula da haramomi biyu masu alfarma na Makka da Madina.

 

3989319

 

captcha