Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, mahukunta a kasar Iraki sun sanar da cewa ana ci gaba da gudanar da dukkanin shirye-shirye dangane da tarukan Ashura na wannan shekara, musammana a birnin Karbala.
Kwamishinan ma'aikatar kiwon lafiya a lardin Karbala Karrar Jawad Abbasi ya bayyana cewa, sun dauki tsauraran matakai na kula da kiwon lafiya a yayin tarukan ashura.
ya ce a halin yanzu an yi wa masu hidima a yayin wannan ziyara a hubbaren Imam Hussain (AS) kimanin mutane dubu 5 allurar rigakafin corona, kamar yadda kuma nan da kafin karshen makon nan sama da mutane dubu 10 za su samu wannan rigakafin daga cikin masu hidima ga maziyarta hubbaren Imam Hussain (AS).
Sannan kuma wadanda suke da shaguna a cikin birnin Karbala da masu ayyuka a otel-otel da wuraren saukar baki, wajibi ne su karbi rigakafin.