A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, mayakan kungiyar Taliban suna ci gaba da kara nausawa zuwa birnin Kabul fadar mulkin kasar Afghanistan da nufin kwace iko da birnin.
Rahoton ya tabbatar da cewa, a ‘yan sa’o’in da suka gabata, mayakan Taliban suna a tazarar kilo mita 50 kawai daga birnin Kabul, kuma sun katse layukan wutar lantarki da suke kai wuta zuwa cikin birnin.
Mai magana da yawun kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid ya sanar a shafinsa an twitter cewa, a daren juiya Jumaa sun kwace iko da babban birnin jihar Arzugan, inda ya ce gwamnan jihar da kuma babban jami’in ‘yan sanda na jihar sun mika wuya ga Taliban.
Hakan nan kuma ya sanar da cewa a jiya sun kwace iko da jihar Zabul, kamar yadda suka kwace iko da babban barikin sojojin gwamnati wanda yake a yankin, kuma tuni dukkanin jami’an gwamnati da suka hada da sojoji da sauran jami’an tsaro da suke yankin suka mika kai ga kungiyar cikin ruwan sanyi.
Rahotanni daga kasar ta Afghanistan dai sun tabbatar da cewa, a halin yanzu manyan biranen jihohi 18 ne suke karkashin ikon Taliban daga cikin jihohi 34 da suke a kasar.
Yanzu haka wasu bayanan na cewa an kafa wasu sojoji sa kai a wasu yankuna na kasar ta Afghanistan daa ciki har da birnin Kabul, domin yin shirin yaki da mayaka kungiyar ta Taliban, wadda take samun nasara cikin sauki wajen kwace yankunan kasar, wadda Amurka da Burtaniya da sauran kasashen kungiyar NATO suka mamaye tsawon shekaru ashirin.
A nasa bangaren kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya bayyana cewa, hakika Iran ta damu matuka dangane da irin yanayin da kasar Afghanistan ta samu kanta a ciki.
Ya ce birnin Harat wanda shi ne birni na biyu mafi muhimmanci a kasar Afghanistan wanda kuma a halin yanzu ya fada karkashin ikon kungiyar Taliban, ya zama wajibi a kan kungiyar da ta bayar da kariya ga ofisoshin diflomasiyya na kasashen ketare da suke a birnin, da kuma kare rayukan fararen hula, da kuma bayar da kariya ga jami’an diflomasiyya na kasashen waje.
Ita ma rundunar sojin kasar Iran ta sanar da cewa, babu wata barazana a kan iyakokin kasar da kuma kasar Afghanistan, komai yana tafiya ba tare da wata matsala ba.
Jamhuriyar musulunci ta kara jaddada kiranta ga dukkanin bangarori a kasar ta Afghanistan, da hakan ya hada da gwamnatin kasar da kuma kungiyar Taliban, da su rungumi hanyar tattaunawa da kuma warware matsalolin kasar ta hanyar yin sulhu da kuma fahimtar juna, tare da dakatar da duk wani abin da zai iya kai kasar ga rushewa.