IQNA

OIC Ta Ce A Shirye Take Ta Taimaka Domin Dawowar Zaman Lafiya A Afghanistan

21:00 - August 15, 2021
Lambar Labari: 3486205
Tehran (IQNA) OIC ta nuna damuwa matuka dangane da halin da kasar Afghanistan ta fada ciki na rashin tabbas.

Kungiyar kasashen musulmi ta bukaci dukkanin bangarorin kasar Afghanistan gwamnati da Taliban da su dakatar da bude wuta, kuma su koma kan teburin tattaunawa.

Kamfanin dillancin labaran Joanna ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyar kasashen musulmi ta fitar a safiyar yau Lahadi, ta bukaci dukkanin bangarorin kasar Afghanistan gwamnati da Taliban da su dakatar da bude wuta, kuma su koma kan teburin tattaunawa ba tare da wani bata lokaci ba.

Bayanin kungiyar ya ce, babu wani abu wanda yake mafita kuma hanyar kawo karshen mawuyacin halin da kasar Afghanistan ta shiga, illa mayar da takubba a cikin kube, kuma dukkanin bangarori su dawo su zauna kan teburin tattaunawa.

Kungiyar ta ce a shirye take ta bayar da dukkanin taimakon da ta rataya a kanta wajen ganin ta hada dukkanin bangarori na siyasa da kabilu da na addini na kasar Afghanistan kan teburin tattaunawa, domin rashin hakan zai iya kai kasar ga fadawa cikin wani yanayi mafi muni dab a a san karshensa.

 

3990784

 

captcha