A rahoton da tashar Russia Today ta bayar, majiyoyin gwamnatin kasar Masar sun tabbatar da cewa, firayi ministan Isra’ila Naftali Bennett ba zai halarci zaman da shugabannin Masar, Falestine da sarkin Jordan za su gudanar a Sharm Al-sheikh ba.
Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, majiyoyin gwamnatin Masar sun sanar da cewa, a yau ne a za a gudanar da zama tsakanin shugabannin Masar Abdulfattah Al sisi, da na Falestine Mahmud Abbas Abu Mazin, da sarkin Jordan Abdullahi na 2, wanda za su gudanar a Sharm Al-sheikh, inda za su tattauna batutuwa da suka shafi wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falastinawa.
A jiya kafofin yada labaran Isra’ila sun sanar da cewa, nan ba da jimawa ba firayi ministan Isra’ila Naftali Bennett zai gana da shugaban kasar Masar AbdulFattah Alsisi a yankin Sharm Al-sheikh na kasar Masar, yayin da wasu ke danganta hakan da zaman na yau.
Sai dai a nata bangaren gwamnatin kasar Masar ta sanar da cewa, a halin yanzu ana tattauna batu yadda za a samu wanzar da zaman lafiya ne tsakanin Isra’ila da Falastinawa, saboda haka maganar ganawa tsakanin Al sisi da Naftali ba ta taso ba a halin yanzu.
Kasar Masar dai na daga cikin kasashen da suka kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila a lokacin mulkin Anwar Sadat, bayan kisan da aka yi wa tsohon shugaban kasar Jamal Abdulnasir, wanda baya dasawa da yahudawan Isra'ila.