IQNA

Putin Na Rasha Ya Caccaki Amurka Kan Matsalolin Da Ta Haifar Wa Mutanen Afghanistan

17:20 - September 02, 2021
Lambar Labari: 3486263
Tehran (IQNA) Shugaba Putin ya ce a cikin shekarun da Amurka ta kwashe tana mamaye da Afghanistan ba haifarwa kasar da wani alhairi ba.

Shugaban kasar Rasha Valadimir Putin ya bayyana cewa, a cikin shekaru 20 da Amurka ta kwashe tana mamaye da kasar Afghanistan, babu wani abin da ta haifar wa kasar na alhairi.

Kamfanin dillancin labarn Sputnik ya bayar da rahoton cewa, a wani jawabi da shugaban kasar Rasha Valadimir Putin ya gabatar a jiya, wanda gidajen talabijin na kasar rasha suka watsa kai tsaye, ya bayyana cewa, dukkanin matsalolin da Afghanistan ta shiga, Amurka ce ta haifar da hakan.

Ya ce Amurka ta shiga kasar Afghansitan ne da sunan tabbatar da tsaro, inda ta mamaye kasar tsawon shekaru 20, amma ba tare da hakan ya tabbata ba.

Putin ya ci gaba da cewa, yanayin da kasar Afghanistan take a ciki yanzu, yana bukatar yin aiki tare a tsakanin dukkanin bangrori na al’ummar kasar, kamar yadda kuma ya ce wajibi ne a kan kasashe masu makwabtaka da Afghanistan da su taimaka ma kasar wajen samun zaman lafiya mai dorewa a cikinta.

Kasar Rasha ta kirkiro wani kwamiti wanda ya hada kasashe masu tasiri a duniya da kuma kasashen yankin, domin taimaka ma kasar Afghanistan, wajen samar da zaman lafiya a kasar, da kuma taimaka ma tattalin arzikinta domin tayar da komadarsa.

 

3994520

 

 

captcha