Jaridar Leadeship ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da bankin musulunci na Jaiz ya bayar, ya sheda cewa, Bankin raya ayyukan ci gaba na musulunci ya saka hannun jari na dala miliyan ashirin da biyar a cikin bankin na Jaiz da ke Najeriya.
Ayman Sejiny babban daraktan gudanarwa na bankin raya ayyukan ci gaba na musulunci ya bayyana cewa, sun saka wadannan kudade a Najeriya da nufin ganin an yi amfani da su wajen bunkasa kananan sana’oi da suka durkushe, ko kuma suka samu koma baya, sakamako bullar cutar corona.
Ya ce bankin yana gudanar da ayyukansa ne a Najeriya bisa yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kansu tare da gwamnatin kasar da kuma sauran bangarori da suke mu’amala da wannan banki, musamman bankin Jaiz, wanda shi ne bankin musulunci a Najeriya.
Tun a cikin shekara ta 2003 ne dai aka kafa bankin Jaiz a Najeriya wanda yake gudanar da ayyukansa bisa ka’idoji na shari’ar musulunci, da suka hada da rashin yin ta’amulli da riba, da kuma kaucewa harkokin kasuwanci da suka shafi abubuwa da aka haramta a muslunci, kamar kasuwancin giya ko abin da ya yi kama da hakan.