IQNA

An Gudanar Da Janazar Allamah Abdulamir Qabalan A Lebanon

20:50 - September 07, 2021
Lambar Labari: 3486281
Tehran (IQNA) a yau ne aka gudanar da janazar babban malamin addini Allamah Abdulamir Qabalan a kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Alahad cewa, a yau an gudanar da janazar babban malamin addini Allamah Abdulamir Qabalan a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Taron janazar dai ya samu halartar jama'a da dama, da suka hada jami'an gwamnati, malamai na addinin muslucni da kuma kiristoci gami da kabilu daban-daban na kasar Lebanon da suka hada da 'yan Duruz da Arman.

A ranar Litinin da ta gabata ce Allah ya yi wa Allamah Qabalan rasuwa bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.

Tun bayan bacewar shugaban majalisar mabiya mazhabar ahlul bait a  kasar Lebanon Imam Musa Sadr, a kasar Libya, bayan da tsohon shugaban Libya Kanal Gaddafi ya gayyace shi, mataimakinsa Allamah Qabalan ya ci gaba da jagorantar lamurran majalisar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron janazar a yau Talata akwai wakilan shugaban kasa da kuma shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon, baya ga haka kuma wasu daga cikin ministoci gami da malaman addini na shi'a da sunnah sun halarci wurin.

Allamah Abdulamir Qabalan dai ya kasance mai goyon bayan hadin kan al'ummar kasar Lebanon, wanda hakan ne ya  bashi matsayi na musamman da girmamawa daga dukkanin al'ummar kasar.

baya ga haka kuma ya kasancea  sahun gaba wajen mara baya ga gwagwarmayar al'ummar kasar wajen yaki da mamayar da Isra'ila ta yiwa kasar har zuwa lokacin da kungiyar Hizbullah ta fattaki Isra'ila daga Lebanon.

 

3995888

 

captcha